Friday, December 5
Shadow

An kayyade naira miliyan 8.5 kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta bayyana cewa an kayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026.

NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar – don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an kayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alkalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.

Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Najeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara.

Karanta Wannan  Kasar Ìràn na mayar da martani me zafi

Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Najeriya – inda ya ce ƙoƙari da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *