Friday, December 5
Shadow

Akwai matsala a sakamakon da muka saki, WAEC tace dalibai su sake duba sakamakon jarabawarsu a yau

Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta WAEC ta bayyana cewa, akwai tangarda a sakamakon data saki a farko.

Dan haka ne ta dakatar da duba sakamakon inda tace a ranar Juma’a dalibai su sake duba sakamakon jarabawarsu.

Hukumar ta sanar da hakanne ta bakin me kula da hulda da jama’ar ta, Moyosola Adesina.

Bayan sakin sakamakon farko, an samu korafi daga iyaye ka yawan faduwar da aka yi jarabawar ta bana inda har wasu ke kiran a soke jarabawar ta bana.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *