
Rahotanni daga jam’iyyar ADC na cewa ana zargin Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da saye duk wani me fada a ji a jam’iyyar da kudi.
Rahoton na jaridar Punchng yace duk sun koma abinda Atiku yake so shi ake yi a jam’iyyar.
Wasu masana harkar jam’iyyar ne suka sanar da jaridar wannan batu amma sun ce kada a fadi sunayensu dan kada a hukutasu.
Saidai me magana da yawun jam’iyyar ta ADC, Bolaji Abdullahi ya musanta wannan zargi inda yace za’awa kowa adalci a jam’iyyar.
Kuma abinda ke gabansu a yanzu shine kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe a shekarar 2027.
Hakan na zuwane bayan da shugaban magoya bayan Peter Obi, Tanko Yunusa ya koka da cewa ba’a yi dasu an mayar dasu saniyar ware a jam’iyyar ADC.
A baya dai an rika rade-radin cewa, Peter Obi zai bar jam’iyyar ADC.