
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata gudanar da sabuwar tantance ma’aikatanta dan fitar da bara gurbi.
Za’a yi tantancewar ma’aikatan ne da aka dauka daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2023.
Babbar sakatariya a ma’aikatar kula da ma’aikatan Gwamnatin tarayya (FCSC), Ndiomu Ebiogeh Philip ta bayyana cewa a wannan karin ba za’a daga yin tantancewar ba kuma duk wanda bai je an tantanceshi ba, za’a bayyanashi a matsayin wanda bai da takardar daukar aiki me kyau za’a sallameshi daga aiki.
Hakan na zuwane a yayin da ake ta siyan aiki da kudi kuma ana zargin takardar aiki da ake baiwa irin wadanda suka sayi aikin ba me kyau bace.