
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, suna aiki tare da kasashen Saudiyya, Amurka, Ingila da sauransu dan samarwa matasa aikin yi a wadannan kasashe.
Ministan Gwadago, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Yace suna horas da matasan wanda zasu je wadannan kasashe su yi aiki kuma abin ya amfane su da kasa baki daya.
Ministan yace yanzu haka suna magana da daya daga cikin kasashen kuma sauran kasashen ma zasu ci gaba da neman wa matasan aikin a can.