Friday, December 5
Shadow

Yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dai-dai ta ƙarkashin Tinubu – Okonjo-Iweala

Yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dai-dai ta ƙarkashin Tinubu – Okonjo-Iweala.

Darakta-Janar ta Hukumar kula da kasuwanci ta duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a ranar Alhamis ta gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda ta yabawa gwamnatin Tinubu kan canje-canje da tayi domin dai-dai ta tattalin arzikin Najeriya.

Okonjo-Iweala wadda ta bayyana ganawar da tayi a matsayin abinda taji daɗi, tace Shugaban Ƙasa ya nuna ya na son zantawa da’ita bayan tabi Uwargidan sa wajen ƙaddamar da kuɗaɗe ga mata.

Kuɗaɗen wanda Hukumar kula da kasuwanci WTO da cibiyar kula da kasuwanci ta duniya ITC da ke Geneva suka samar, nada nufin haɓɓaka kasuwanci da samar da ayyukan yi da samar da kuɗaɗen shiga ga mata.

Karanta Wannan  'Yan majalisar Dattijai sun tafi hutun wata biyu

Daga Usman Salisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *