Friday, December 5
Shadow

Zuwa yanzu, Shugaba Tinubu ya shafe kwanaki 181 a kasashen waje tun bayan hawansa mulki

Jam’iyyar ADC ta caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen waje.

Jam’iyyar ta bayyana hakane ta bakin kakakinta, Bola Abdullahi inda yace ana kashe kudaden Talakawa wajan tafiye-tafiyen shugaban kasar.

Ya bayyana cewa, wannan shine karo 40 da shugaba Tinubu zai bar Najeriya tun bayan hawansa mulki kuma ya kwashe kwanaki 181 a kasashen waje.

Sanarwar tace wannan kusan watanni 6 kenan da shugaba Tinubu ya kwashe a kasashen wajan.

ADC tace tana Allah wadai da irin wadannan tafiye-tafiyen na shugaban kasa musamman ganin cewa babu wani abin ci gaba da hakan ya kawowa kasarnan.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda Ya Yi Haɗãri, Ya Samu Rãuɲi A Ƙafa, ji Halin da yake ciki a yanzu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *