
A jiyane aka daura auren Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Amaryarsa, Maimuna Musa.
Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda aka kaishi dakin amaryarsa.
Tuni ‘yan Uwa da abokan Arziki suka rika taya Adam A. Zango murnar aurensa.
Amarya Maimuna dai ta yi fatan Allah yasa mutuwa ce zata rabata da gidan mijinta.