
Kokarin gano wanene ainahin mijin Rahama Sadau ya faskara inda akai ta yada hotunan mutane daban-daban ana cewa sune suka aureta amma daga baya a gano cewa ba gaskiya bane.
Tun bayan daura auren Rahama Sadau da mijinta me suna Ibrahim ake ta kokarin ganin mijin amma abu ya gagara.
‘BBCHausa sun ce Rahama Sadau ta tabbatar musu da cewa ta yi aure.
Hakanan ‘yan uwan Rahama Sadau duk sun tabbatar da cewa ta yi aure.
Yawanci ba’a san da maganar auren Rahama Sadau ba sai ranar da aka daura auren.
Dan uwan Rahama Sadau, Haruna ya shaida cewa sun yi dabarar cewa kanwar Rahamar, Fati ce zata yi aure dan a kawar da hankalin mutane.
Abubuwan da suka sa wasu ke tababar auren Rahamar sune:
Ba’a ga mijinta ba.
Ba’a san da auren nata ba sai ranar auren.
Ba’a yi wani gagarumin shagali ba.
Wannan magana dai ana iya cewa ra’ayin masu itace, watau ba gaskiya bane, domin duka alamu sun tabbata cewa Rahama Sadau ta yi aure.
Har Bidiyon daurin auren Rahama Sadau ya yadu sosai.