Wasu malaman makaranta a kasar Amurka sun yi ritaya bayan da aka kamasu suna yunkurin yin taron dangi dan yiwa dalibinsu fyade.
Malaman mata sunansu Alexsia Saldaris da kuma Jennifer Larson dake koyarwa a makarantar Joseph Craig High School dake garin Janesville dake jihar Wisconsin.
An gano cewa, daya daga cikin malaman har ta aikewa da dalibin hotonta na batsa.
Bayan da aka tunkareta da maganar, ta amsa cewa lallai ta aikawa da dalibin hotunan batsa.
Hakanan sun kuma nemi dalibin ko zai sako musu karin wani dalibi ya zo su yi lalatar tare dashi.
Yanzu haka dai hukumar ‘yansanda ta garin Janesville tana bincike kan lamarin.