
Wani dan Najeriya me suna Idris Ayo Bello ya bayyana yanda da ya halarci wajan taron ci gaban Afrika da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan da kuma abin kunyar da ya gani.
Yace wajan da aka warewa Najeriya ta tsaya babu kowa a wajan.
Yace da ya ga abin yayi yawa, shine da kansa ya je wajan ya tsaya ya kuma rika amsa tambayoyi akan kasuwancin Najeriya da ci gabanta da wasu ‘yan kasashe ke yi.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya halarci wajan taron, kuma rahotanni sun bayyana cewa, an tanadi mutanen da zasu tsaya a irin wannan waje dan wakiltar Najeriya.