
Zuwa yanzu dai an saka Asibitin Malam Aminu Kano dake Kano cikin asibitocin gwamnatin tarayya ta aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira dubu 12.
A baya dai an samu suka ga gwamnati bayan data sanar da ragin kudin wankin kodar a asibitocin Gwamnatin tarayya ba tare da hadawa da asibitin malam Aminu Kano ba.
Lamarin ya jawo cece-kuce sosai musamman a kafafen sada zumunta.
Saidai a cewar tsohon Hadimin Gwamnan Kano, Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana cewa, yanzu an saka Asibitin malam Aminu Kano cikin wadanda akawa ragin.