
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Dalilin da yasa ba’a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a wajan taron ci gaban kasashen Afrika a kasar Japan ba, wakilan Najeriya sai ranar Alhamis zasu isa wajan.
Rahotanni sun watsu cewa, babu wakilin Najeriya a wajan inda sai wani dan Najeriya ne da ya halarci taron kuma abin bai masa dadi ba ya gabatar da kansa a matsayin shine ke wakiltar kasar.
Saidai a bayanin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya halarci wajan taron, Bankin masana’antu, Bank of industry ya halarci wajan taron,
Ministan wuta, da sauran manyan ma’ikatan gwamnati duk dun halarci wajan taron amma duk suna can suna ganawa da wakilan kasuwanci da zai amfani Najeriya.
Ya kara da cewa, wadanda zasu tsaya a wajan da aka warewa Najeriya sai ranar Alhamis zasu je kasar ta Japan.
Yace dan haka Najeriya ta samu wakilci sosai a wajan taron.