Friday, December 5
Shadow

Gidajen Man fetur din Najeriya A.A Rano, Total, Mobil, sun rage farashin man fetur dinsu a Abuja

Gidajen man fetur din Najeriya irin su AA Rano, Total, Mobil, NIPCO duk sun rage farashin man fetur dinsu dan yin gasa da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL da sauransu.

Saidai ragin ya farune a Abuja da kewaye kadai.

Gidajen man fetur din AA Rano, Ranoil, Mobil, da NIPCO sun rage farashin man su zuwa Naira 890 akan kowace lita maimakon Naira 945.

Suma gidajen man fetur din Empire Energy, Emadab, da Total duk sun rage farashin man fetur dinsu inda wasu ke sayarwa akan naira 899 wasu kuma 910 akan kowace lita a Abuja.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Abubakar Maigandi ya bayyana cewa sun rage farashinne saboda faduwar farashin danyen man fetur da kuma raguwar farashin man a inda suke sarowa.

Karanta Wannan  Kalli Sabon Bidiyon Dan majalisa Alhassan Ado Doguwa a Landan yana Kwambo daya dauki hankula inda a wannan karin aka ganshi yana cin abinci a bandaki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *