
Sanata Ahmed Wadada, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, ya fice daga jam’iyyar SDP.
Murabus ɗin nasa ya fito ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar na gundumar Tudun Kofa, ƙaramar hukumar Keffi, Jihar Nasarawa.
“Ina mai rubuta wannan wasiƙa ne don sanar da ku shawarar da na ɗauka ta ficewa daga kasancewa ɗan jam’iyyar SDP, daga yau nan take. Wannan shawara ba a ɗauke ta da sauƙi ba, amma na ji tilas in ɗauki wannan mataki saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna addabar jam’iyyarmu,” in ji shi.
Ya ce rikice-rikicen cikin gida sun jawo rabuwar kai sosai da kuma shari’o’i a tsakanin jam’iyyar.
Wadada ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake memba, tare da bayyana farin cikinsa kan gogewa da alaƙar da ya samu.
Sai dai, sanatan bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.
TheCable ta rawaito cewa a ranar 13 ga watan Agusta, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, Wadada ya shaida wa manema labarai cewa babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin tsarin haɗin gwiwar ADC da zai iya yin takarar daidai da Tinubu dangane da ayyukan da ya gudanar a mulki.