Friday, December 5
Shadow

Ganduje ya dawo daga London bayan ya shafe wata domin neman lafiya

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya daga Landan a jiya Laraba.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya tafi ƙasar Birtaniya domin neman magani jim kaɗan bayan murabus ɗinsa daga shuagabancin jam’iyya mai mulki a ƙasar.

Da ya ke tabbatar da wannan batu ga jaridar The PUNCH, tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammed Garba, ya ce Ganduje ya sauka a Nijeriya ne a safiyar jiya Laraba bayan shafe kusan wata guda a waje.

“Eh, ya dawo Najeriya yau. Ya dawo cikin koshin lafiya, kuma ya ƙarasa gidansa,” in ji Garba, yayin da ya ke tabbatar wa da jaridar PUNCH.

Ya ƙara da cewa Ganduje ya bar Najeriya zuwa Landan ne kwana biyar bayan ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar domin neman lafiya.

Karanta Wannan  Da Duminsa: A karshe dai Hukumomin Saudiyya sun amince a binne gawar marigayi, Aminu Dantata a Madina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *