Sunday, September 6
Shadow

Rundunar sojin Najeriya ta ce kiran kare kai ba ya nufin mallakar makami

Shalkwatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin haske kan kalaman da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi kan batun kare kai daga hare-haren ƴan fashin daji.

Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ta fitar ta ce kalaman Janar Musa ba suna ƙarfafa wa mutane mallakar makami ba ne, kamar yadda wasu kafofin labarai a ƙasar ke yaɗawa.

”Abin da yake nufi shi ne ƴan ƙasa su koyi dabarun kare kai da duniya ta amince da su kamar ƙwarewar tuƙi, da judo da ninƙaya da dambe ko kokawa da sauransu”, in ji sanarwar.

”Kalamansa ba sa nufin mallakar makami ta haramtacciyar hanya, saboda yana sane da dokokin Najeriya da suka haramta mallakar makami”.

Karanta Wannan  Allah Sarki,Kalli Bidiyo gwanin ban tausai, Sun dauke ta da niyyar aikata Alfasha, Ashe matsayafa ne, duk da tana rokonsu su yi hakuri, sun mata Tsyrara suka aikata inda ba'a dawowa dan yin tsyfin kudi

A ranar Alhamis ne cikin wata hira da gidan Talbijin an Channels, Janar Musa ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarun kare kai domin kauce wa hare-haren ƴanbindiga.

Kalaman babban hafsan dai sun janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan ƙasar inda wasu ke ganin hakan na nuna gazawa a ɓangaren gwamnati na magance matsalar rashin tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *