Friday, December 5
Shadow

Duk da kokarin shugaba Tinubu na rage farashin magunguna a Najeriya, Farashin Magungunan sai kara tashi suke

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi yunkurin rage farashin magunguna a Najeriya dan samarwa musamman talakawa da masu karamin karfi saukin rayuwa.

Saidai duk da wannan, ana ci gaba da samun hauhawar farashin magunguna.

A watan Yuni na shekarar 2024 ne Ministan Lafiya,Muhammad Pate ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire haraji akan magunguna da ake shigowa dasu Najeriya da kayan aikin hada magunguna, musamman dan a saukaka farashin hada magungunan a Najeriya.

Saidai rahoton jaridar Punchng yace har yanzu magunguna irin na su hawan jini da zazzabin cizon Sauro da sauransu ba su yi sauki ba.

Karanta Wannan  Asibitin koyarwa na Jami'ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *