Friday, December 5
Shadow

Sai na rage wa Tinubu ƙuri’a miliyan guda a 2027 – Kabiru Marafa

Tsohon Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin rage wa Tinubu ƙuri’u masu yawa a zaɓen 2027.

Marafa, wanda a baya-bayan nan ya sanar wa BBC ficewarsa daga jam’iyyar APC, bayan ya zargi Tinubu da ”watsar da shi bayan cin zaɓe” ya ce sai ya kawo wa shugaban ƙasar cikas a zɓen 2027 da ke tafe.

Yayin wata hira da hgidan talbijin na Channels, Sanata Marafa ya ce sai ya janyo wa Tinubu asarar kimamin ƙuria’ miliyan guda.

Tsohon ɗan majalisar – wanda ya kasance babban daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu a Zamfara a 2027 – ya ce zai nuna wa shugaban ƙasar matsayinsa a siyasar jihar Zamfara.

Karanta Wannan  Ana shirin sasanta Kwankwaso da Ganduje da Shekarau 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *