
Matashiya daga Arewa, me suna Fatima ta bayyana cewa, babu wanda take so Duniyarnan sai shahararren dan fafutuka na kudu VDM.
Ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok inda aka ga ta wallafa Bidiyo tana kuka tana cewa shin wai me yasa mutane suka kasa fahimtarta?
A wasu abubuwa data wallafa a shafinta na Tiktok, Hutudole ya hango inda take cewa ita matarsa ce.
Da yawa dai na gaya mata cewa hakan ba zai yiyu ba saboda ita musulma ce shi kuma ba musulmi ba.
Saidai tace ita idonta ya rufe akan VDM.