
Tsohon karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya bayyana cewa, babu yanda bai yi da tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ba kan a kara kudin man fetur amma yaki.
Yace Buhari ya ki a kara kudin man fetur ne saboda tausayin talakawa da yake dashi.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
Kachikwu yace amma daga baya Buhari ya amince inda yace a fara maganar cire tallafin man fetur saidai Ministan yace Buharin yace masa idan hakan bai haifar da da me ido ba, zai sallameshi daga aiki.