
Rahotanni sun ce, Mele Kolo Kyari, tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, na can hannun hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC inda yake amsa tambayoyi
Kyari ya kai kansa ofishin hukumar ne ranar Laraba.
Sannan ana masa bincikene kan kudaden da aka ware dan gyaran matatun man fetur din Najeriya.
Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta tabbatar da tambayoyin da akewa Mele Kolo Kyari.
A baya dai kotu ta kulle asusun ajiyar banki na Mele Kolo Kyari bayan da EFCC ta bukaci hakan.