
Hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta maka mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore a kotu bisa zarginsa da kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me laifi.
Sannan an zargi Sowore da kuma bayyana shugaban kasar a matsayin makaryaci saboda yace yayi ikirarin magance matsalar rashawa da cin hanci a kasar Brazil amma Sowore yace maganar ba gaskiya bace.
Sowore ya wallafa cewa DSS na shirin kaishi kotu kuma a shirye yake idan an kaishi Kotun ya ansa gayyata.