
Tsohuwar hadimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta bayyana cewa, ziyarar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihar Kaduna bata yi Armashi ba.
Ta godewa mutanen Kaduna saboda kin fitowa su tarbi shugaban kasar inda tace sai yara aka samo aka zuba akan titi.
Ta bayyana hakane a shafinta na X.
Ta kara da cewa, wannan sakamakon mulki da rashin bin doka kenan.