Friday, December 26
Shadow

Akwai yiyuwar Tinubu ba zai so sauka daga Mulki ba, zai so ci gaba da zama shugaban Najeriya har karshen rayuwarsa>>Inji El-Rufai

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi gargadi cewa muddin ‘yan Najeriya basu tashi tsaye ba suka yi abinda ya kamata a 2027 ba, to lallai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai so ya zarce ya mulki Najeriya har iya tsawon rayuwarsa.

El-Rufai ya kwatanta Abinda Tinubu ke son yi da irin mulkin shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.

El-Rufai yayi wannan maganane a yayin da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai masa ziyarar jaje bayan tarwatsa taron ADC da aka yi a Kaduna.

El-Rufai yace ko mulkin Soja bai ga ana yin irin kamar karyar da Gwamnatin Tinubu ke yi ba

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Dan haka yace dolene a hada kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *