
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, ba kamar yanda ake yada jita-jita ba wai Hausawa da Fulanine zasu fi rike manyan mukamai a gwamnatinsa ba, Yarbawa zai fi baiwa mukamai.
Atiku ya bayyana cewa, Matarsa ta Farko, Bayarbiyace kuma suna da ‘ya’ya 4 da ita.
Yace Yarbawa na da matsayin na kusanci irin na ‘yan uwantaka a wajansa.
Hakanan yace yana girmamasu sosai, kamar yanda kafar voicenews.com.ng ta ruwaito