
Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, Magoya bayan shugaban kasar, Paul Biya na yakin neman zabe da hotonsa ba tare da shi ya halarci wajan yakin neman zaben ba.
Paul Biya me shekaru 92 a Duniya ya sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zaben shugaban kasa da za’a gudanar nan da watan Oktoba.
Biya a yanzu shine shugaban kasa mafi tsufa a Duniya kuma shine na biyu wanda yafi dadewa akan kujerar mulki a nahiyar Afrika.
Rahotanni sunce ana ta yama didin bashi da lafiyane shiyasa ya kasa halartar wajan yakin neman zaben.
Paul Biya dai ya sha fita zuwa kasashen waje wajan neman lafiya.