
Gwamnan rikon Kwarya na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas wanda ya shafe watanni 6 a mukamin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadarsa dake Abuja da yammacin jiya, Laraba.
Rahotanni daga Punchng sun ce ganawar ta samu halartar Ministan kudi, Wale Edun da kuma shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode.
Saidai ba’a samu bayani kan abinda suka tattauna ba.
Hakan na zuwanw kwanaki 3 bayan da Ibas yace bai yadda da shirin binciken da majalisar jihar Rivers ke shirin yi masa ba inda yace Bincikensa kamar binciken shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne da majalisar tarayya domin shi Tinubu ne ya bashi aiki.
Rahotanni sun ce Jihar Rivers me arzikin mai ta samu makudan kudaden shiga da suka Haura daruruwan Biliyoyin Naira a watanni 6 da Ibas yayi na gwamnan rikon kwarya.