
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gargadi kiristoci masu son tafiya jeru salem Ibada cewa kada wanda ya makale a can yaki dawowa Najeriya.
Shugaban yace babu kasar data kai Najeriya ‘yanci da dadi musamman idan mutum na zaune a wata kasar ba bisa ka’ida ba.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume a yayin da kiristocin ke shirin tafiya aikin ibadar.