
Malamin Addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa yunwa ba uzuri bane ga mace ta aikata zina ko kuma tace wai dan ‘ya’yanta su yi makaranta duk bai halatta ba.
Yace a guri daya ne kawai ya halatta mace ta aikata Zyna shine idan aka ce za’a kasheta idan bata yadda ba.
Malam ya bayyana hakane a wajan karatun da yakevna ranar Juma’a da yamma a masallacin Sultan Bello dake Kaduna, kamar yanda wakilin hutudole ya halarta.