Friday, December 26
Shadow

Lamari Ya Munana: Kungiyar PENGASSAN dakatar da ayyukan tace mai a matatar Man fetur ta Dangote

Rahotanni sun tabbatar da cewa Kungiyar PENGASSAN ta manyan ma’aikatan man fetur ta dakatar da aikin tace man fetur a matatar man Dangote.

Rahoton yace A yanzu ayyuka sun tsaya cik a matatar man fetur din.

Hakanan lamarin ya shafi bangaren yin takin zamani.

Saidai PENGASSAN tace ta bar wani bangare na Gas a ma’aikatar dake aikin kaso 60 cikin 100.

Matatar ta dauki wannan mataki ne dan matsawa masu gudanarwa na matatar su mayar da ‘yan Najeriya 800 da aka kora aiki saboda shn shiga kungiyar ta PENGASSAN.

PENGASSAN ta dauki wannan mataki ne a ranar Lahadi bayan data fara yajin aikin sai abinda hali yayi.

Karanta Wannan  Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa matsalar Talauci>>Inji Gwamnan Anambra

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *