
Hukumar kula da cutuka ta kasa, NSCDC ta bayyana gargadi ga ‘yan kasa bayan da cutar zubar da jini, Ebola ta sake bayyana a kasar uganda.
Shugaban hukumar ta NCDC, Jide Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar.
Cutar Ebola dai tana yaduwa ne a tsakanin Al’umma ta hanyar taba jikin me ita ko jininsa ya taba naka ko sauran ruwan dake fita daga jikin dan Adam.
Jide Idris yace duk da yake cutar bata kai ga zuwa Najeriya ba amma suna kokarin ganin bata shigo kasar ba inda suka hada hannu da hukumomin da abin ya shafa.