Friday, December 5
Shadow

Majalisar Shura za ta watsa zama da Sheikh Lawal Triumph kai tsaye

Sakataren Majalisar Shura ta Kano, Shehu Wada Sagagi ya ce da farko za a fara da aike masa takardar gayyata tukunna wadda kuma za ta ƙunshi rana da lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin.

Ya kuma ƙara da cewa domin cire shakku daga zukatan al’umma an shirya yin zaman kai tsaye.

“Wannan zama an shirya yin sa ne “Live” wato kai tsaye domin kowa ya ga irin tambayoyin da za a yi masa da kuma irin amsoshin da zai bayar,” in ji Shehu Sagagi.

Dangane kuma da labaran da ke yawo a kafafen watsa labarai kan cewa Majalisar ta dakatar da Malam Lawal Triumph daga yin wa’azi, sai Shehu Sagagi ya ce a’a ba wai an hana shi yin wa’azi ba ne kwata-kwata.

Karanta Wannan  Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar

“E an kawo shawara ne cewa wasu mutane suna ta fitintunu ana ta maganganu marasa daɗi har daga wajen jihar da ake ganin wannan abun zai iya hargitsa gari saboda haka aka kawo shawarar cewa a dakatar da shi daga dukkan waɗannan maganganu da suka shafi wannan mas’ala.” In ji Sagagi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *