
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, yawan ‘yan Najeriya da ake da su zai iya karuwa zuwa Miliyan 400 nan da shekarar 2050.
Obasanjo ya bayyana hakane yayin bude wani sabon gurin kimiyya da Fasaha a jihar Sokoto.
Yace nan da shekaru 25 idan ‘yan Najeriya suka karu suna bukatar aikin yi da abinci wanda idan basu samu ba, hakan zai iya kawo matsala.
Yace hanya daya ce ta magance wannan matsala itace tun yanzu a baiwa matasa masu tasowa Ilimi.
Yace idan kuwa ba haka ba, matsalar tsaron da za’a fuskanta nan gaba tafi wadda ake ciki yanzu.