Thursday, February 5
Shadow

Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahotanni dake yawo cewa wai yace zai janye wa matashi yayi takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC.

Atiku ta bakin me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wannan magana ba gaskiya bace.

Yace a hirar da yayi da BBC babu inda yace zai janyewa wani dan takara, yace abinda ya fada shine idan aka yi zaben fidda gwani kuma matashi yayi nasara a zaben zai goya masa baya.

Atiku yayi kira ga ‘yan Jarida su daina fassara labari ba yanda ya kamata ba.

Karanta Wannan  Hukumar Sojojin Najeriya ta Hana manyan Sojoji auren 'yan kasar waje da Kuratan Sojoji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *