
Hukumomin ‘yansanda sun kama sanata Elisha Abbo Saboda zargin aikatawa wata yarinya Fyade.
Rahoton yace Tsohon sanatan wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa ya mika kansa wajan ‘yansanda a Abuja bayan da aka zargeshi da yiwa yarinya me shekaru 13 fyade.
Iyayen yarinyar sun yi zargin cewa, sanata Senator Aishatu Dahiru Ahmed (Binani) ta je har gidansu inda ta rokesu da kada su fitar da maganar.
Hakanan shima sanata Elisha Abbo ya rika aikawamahaifin yarinyar kudade da shirin kulle musu baki.
Dan Rajin kare hakkin bil’adama kuma Lauya, Deji Adesogan ne ya bayyana hakan sannan yace har yanzu sanata Elisha Abbo na daure a hannun ‘yansanda.
Wannan dai ba shine karin farko da Sanata Elisha Abbo ya shiga karma-karma ba, a baya ya taba cin zarafin wata mata a ofishin sayar da kayan biyan bukatar jima’i a Abuja.