Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa bata nace akan sai gwamnatin tarayya ta biya naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi ba.
Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa dashi.
Yace a shirye suke su amince da kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin (250,00) a matsayin mafi karancin Albashin.
Gwamnatin tarayya dai bata bayyana matsayar ta ba kan mafi karancin albashin ba.