
Tsohon dansandan Najeriya me mukamin DSP ya koka game da yanda yace an kasa biyansu hakkokinsu bayan sun kwashs Shekaru 35 suna aiki.
Yace a lokacin da suke aiki, sune suka rika raka ‘yan siyasa da kudaden da suka sata zuwa kauyukansu suna boyewa, yace amma gashi sun gama aiki biyansu hakkokinsu ya gagara.
Ya bayyana hakane a wajan zanga-zangar neman hakokinsu da suka fito.