
Babban bankin Najeriya, CBN ya saka sabbin dokokin hadahadar kudi na POS.
CBN ya bayyana sabbin dokokin wanda yade dolene kowa da lamarin ya shafa ya tabbatar yana wa dokokin Biyayya.
Daya daga cikin dokokin da suka fi daukar hankali itace wadda tace a kullun an Amincewa dan POS ne yayi hadahadar kudi da bata wuce Naira Miliyan 1.2 ba.
Wasu dai na ganin wannan doka da wuya ta yi aiki domin mutum daya zai iya mallakar POS daban-daban fiye da daya.