
Manhajar sada zumunta ta WhatsApp zasu daina amfani da lambar waya wajan gane mutum.
WhatsApp zasu koma amfani da Username inda hakan wani mataki ne na baiwa mutane sirri.
Tuni Rahotanni suka bayyana cewa, an fara gwajin hakan amma ba’a bayyanashi ga sauran Al’umma ba.
Nan gaba kadanne ake tsammanin kowa zai fara amfani da wannan sabon tsari da zarar an kammala gwajinsa.