Friday, December 5
Shadow

Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar II ya nemi Gwamnati ta yi dokar sanya ido a kafafen sadarwa saboda chin Mutuncin da ake yiwa manyan mutane yayi yawa

Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya nemi Gwamnati data yi sabuwar dokar da zata rika saka ido a kafafen sada zumunta saboda cin fuskar da akewa manyan mutane ta yi yawa.

Hakanan ya bayyana cewa ana amfani da kafafen sada zumuntar dan barazanar tsaro.

Yace amfani da kafafen sadarwa ta hanyar da bata kamata ba na barazana ga zaman lafiya, Girmama juna, da hadin kan kasarnan.

Ya bayyana hakane ta bakin Me martaba sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli a wajan taron manyan malamai daya gudana a Kaduna wanda aka yi saboda tattauna matsalar tsaro da zaman takewa.

Yace a wasu kasashen akwai dokar amfani da kafafen sadarwa ta yanda idan mutum ya saka sakon da bai kamata ba ko na cin zarafi za’a nemoshi a hukuntashi.

Karanta Wannan  Bidiyo: An yi kuskuren turawa Fasto Naira Miliyan 1 mimakon dubu dari a matsayin sadaka saidai da aka ce ya mayar da kudin, yace Kudin da aka baiwa Yesu sadaka ba'a mayar dasu, me kudin ya kira 'yansanda

Yayi kira ga mahukunta dasu dauki irin wannan mataki a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *