
Shugaban Rundunar tsaron Najeriya, Christopher Musa ya bayyana cewa Sulhu ba zai yi aiki a yaki da ‘yan Bindiga ba.
Yace kokarin yin sulhu bata lokaci ne kawai, ba zai taba cimma abinda ake so ba.
Yace Gwamnatocin jihohin basa basu hadin saboda kowace jiha na da irin salon da take son yin amfani dashi dan magance matsalar.
Yace abinda ‘yan Bindigar kawai suke so shine Mulki, Kudi, da barzana ga mutane, Kamar yanda Idris4peace ya ruwaito.