
Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana takaici kan yanda yanayin lalacewar tarbiyya musamman da yawaitar zinace-zinace suka yi yawa a tsakanin al’umma.
Malam ya bayyana hakane a yayin wa’azin da ya gudanar na Mukhtasar Khalil a masallacin Sultan Bello dake Kaduna Ranar Juma’a.
Malam yace Al’ummar Arewa da aka santa da Kunya da kawaici Yau Tiktok yasa mata sun zama marasa kunya.
Malam yace a Arewa ne aka samu wata mace tace Minista ya mata ciki ya kuma ki daukar nauyin dan.
Yace hakanan a Arewa ne aka samu wani ma’aikacin Kwastam da mata 3 a dakin Otal ya mutu.
Yace dole Allah ya jarrabemu.