
Wani mutum dan jihar Delta me suna Emmanuel Efayeta Kuejubola ya aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da budaddiyar wasika inda yake neman shugaban kasar ya bashi bashin Naira Biliyan 12.
Yace burinsa shine ya gina gidaje 400 masu dakina 2 a jiharsa ta Delta.
Yace idan aka bashi bashin, nan da watanni 36 zai mayar da kudin ya biya bashin.
Yace a baya ya taba aikawa Dangote irin wannan wasika amma bai sami amsa ba.
Yace yana fatan a wannan karin zai samu amsa daga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.