
Tsohuwar hadimar shugaban kasa a zamanin Mulkin shugaba Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta bayyana cewa ashe maganar juyin mulkin gaskiyace.
Tace shiyasa suka ga manyan kasar hadda shugaban kasa sun tafi kasashen waje ta yanda idan an yi juyin mulkin zasu samu sauki.
Ta bayyana hakane a shafinta na X.
Hakan na zuwane bayan da Sahara reporters ta ruwaito cewa, an kama wasu janarorin soji 16 da suka yi yunkurin yiwa Gwamnatin Tinubu juyin mulki.