Friday, December 5
Shadow

Sabon Rahoton ya yi bayani dalla-dalla yanda wasu sojoji suka so yiwa shugaba Tinubu juyin mulki, Sun so su aika shugaba Tinubu, Kashim Shettima, Akpabio da Tajudeen Abbas Qhiyama

A baya mun samu rahoto daga Sahara reporters cewa an kama wasu sojoji 16 da suka yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.

Duk da hukumar sojoji tace sojojin sun aikata wasu laifuka ne na rashin da’a, Saidai Sahara reporters tace juyin Mulki ne sojojin suka shirya amma ake boye maganar.

Hakanan kafar Premium times itama ta tabbatar da cewa aojojin sun shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin mulki ne.

Hakanan an kamasu ne tun kamin ranar 1 ga watan October, sannan su kusan 20 ne a cewar Sahara reporters

Hakanan premium times tace sojojin sun shirya yin juyin mulkinne ranar 25 ga watan October inda suka so kashe ahugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio, dana wakilai, Tajudeen Abbas.

Karanta Wannan  Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana'a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Sannan sun so kama manyan hafsoshin tsaro na kasarnan.

Sun kuma yi aiki ne tare da wasu dake taimaka musu da bayanai daga fadar shugaban kasa.

Saidai Premium times tace tuni aka kama sojojin aka kuma kafa kwamitin da zai bincikesu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *