
Tauraruwar fina-finan Hausa, Princess Mufida ta Kwana Casa’in ta wallafa wasu hotuna a shafinta na sada zumuntar Instagram wanda suka jawo cece-kuce sosai.

Hotunan dai sun nuna ta babu riga ko rigar mama wanda wasu suka rika cewa tsirara take.

Wasu kuwa sun rika fatan ganin hoton dukanshi.

Saidai Mufida a kasar Hoton ta rubuta cewa na AI ne amma duk da haka mutane na ta mata Allah wadai.