
Majalisar Dattijai ta nemi a karawa sojojin Najeriya Albashi musamman lura da yanayin tsadar rayuwa da kasarnan ke ciki.
Majalisar tace ya kamata a karawa sojojin dake sadaukar da rayuwarsu dan baiwa kasarnan kariya Albashi.
Hakannna zuwane kasa da sati daya da bayyanar rahotannin yunkurin juyin mulki da ke cewa an kama sojoji 16 dake da hannu a lamarin.