
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, a lokacin da ya so sauka daga Mulki, an bashi shawarar ya dauko Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin magajinsa.
Yace amma a wancan lokacin yaki yadda da wannan shawarar.
Yace dalili kuwa shine yace Sai El-Rufai ya kara hankali.
Yace da wanda ya bashi shawarar ya ga irin ayyukan El-Rufai yake yi shine ya sake zuwa ya sameshi yace lallai ya yadda da maganarsa.
El-Rufai dai yayi ministan Abuja a zamanin mulkin Tsohon shugaban kasar.