
Dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a Labour Party Peter Obi ya bayyana cewa, masu damfarar yanar gizo, Wanda aka fi sani da Yahoo Boys mutanene masu basira.
Yace ida aka kula dasu aka canja musu tunani zasu amfani ci gaban kasa.
Ya bayyana hakane a Onitsha Jihar Anambra ranar Asabar.
Ya yi kiran da a daina karfafa cin hanci da Rashawa a Najeriya.